Jarumar KannyWood, Rashida Mai Sa’a Tayi Aure

Rashida Mai Sa’a, tsohuwar mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan harkokin mata, Abdullahi Umar Ganduje, kuma tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood, ta yi aure. Ita ce kuma shugabar kungiyar jaruman mata ta Kannywood (AKAFA).

Labarin aurenta ya bazu a shafukan sada zumunta a wannan makon, inda katin auren ta ke yawo.

Rashida Mai Sa’a ta shahara a masana’antar Kannywood, inda ta kasance cikin fitattun jarumai a lokacin da take shirya fina-finai. Don haka ne aka nada ta a matsayin mai ba da shawara kan harkokin mata a zamanin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.