Jaruma Maryam Yahya Ta Ziyarci Filin Wasa Na Arsenal

Shahararriyar jarumar Kannywood Maryam Yahaya ta raba kayatattun hotunan ta a filin wasa na Emirates Arsenal da ke birnin Landan na kasar Ingila. Filin wasa gidan shahararren kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ne.

Jarumar ta fito a wajen filin wasa na Emirates sanye da koriyar rigar Arsenal. Masoyan ta a Instagram sun yi mamakin hotunanta inda suka fara tattaunawa mai dadi.

Maryam Yahaya ta kuma ziyarci wasu wurare da dama a nahiyar Turai a wani bangare na rangadin da ta yi. Ta saka karin hotunan tafiyarta a shafinta.