JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar UTME
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta fitar da sakamakon jarrabawar da aka yi a shekarar 2022 ta Mock da jarrabawar gama gari (UTME) da aka gudanar a ranar 9 ga watan Afrilu.
JAMB ta bayyana haka ne a cikin sanarwar ta na mako-mako na ofishin magatakardar hukumar, ranar Litinin a Abuja.
“Saboda haka, yan takarar da suka zana jarrabawar za su ziyarci www.jamb.gov.ng su danna ‘2022 Mock Result Checking’ su shigar da lambar rajistar UTME don samun sakamakon su,” inji shi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa akalla dalibai 175,000 ne suka zana jarrabawar a cibiyoyin JAMB 757 a fadin kasar.
Magatakardar hukumar Farfesa Is-haq Oloyede, wanda ya zanta da NAN bayan gudanar da atisayen a ranar Asabar, ya bayyana jin dadin shi kan yadda ake gudanar da jarabawar a fadin kasar.
Oloyede yace yan takara 175,000 da suka rubuta jarabawar ba’a, an takaita su ne kawai a zama daya kawai wanda aka fara daga karfe 8 na safe zuwa karfe 10 na safe.
Ya kuma ba da tabbacin cewa hukumar da dukkan cibiyoyin gwajin na’urar kwamfuta (CBT) sun shirya don gudanar da babban jarrabawar 2022 da ke tafe daga ranar 6 ga Mayu zuwa 16 ga Mayu.
NAN ta ruwaito cewa an yiwa mutane miliyan 1.8 rijista don babban UTME na bana. (NAN)