Itaciyar Tuffan Mu: Labari Mai Sosai Zuciya

Da dadewa, akwai wata katuwar Itaciyar tuffa (Apple). Wani karamin yaro yana son zuwa yayi wasa a kusa da Itaciyar kullun. Ya hau saman bishiyar, ya ci tuffa, ya huta a ƙarƙashin inuwar.

Yana son bishiyar kuma Itaciyar yana son wasa da ita. Lokaci ya wuce, ɗan yaron ya girma kuma ya daina wasa a kusa da Itaciyar kowace rana.

Watarana yaron ya dawo kan bishiyar sai yayi bakin ciki.

“Zo ka yi wasa da ni”, bishiyar ta cewa yaron.

“Ni ba yaro ba ne, ba na wasa a kusa da bishiyoyi” yaron ya amsa.

“Ina son kayan wasan yara. Ina bukatan kudi domin in sayo su.”

“Yi hakuri, amma ba ni da kuɗi, amma za ka iya debo tuffana duka ka sayar da su. Don haka, za ka sami kudin.”

Yaron yayi murna sosai. Ya dakko tuffa da ke kan bishiyar ya tafi da murna. Yaron bai dawo ba bayan ya debi tuffa. Itaciyar tayi bakin ciki.

Watarana yaron da yanzu ya koma mutum ya dawo sai bishiyar tayi murna.

“Zo ka yi wasa da ni” bishiyar ta ce masa.

“Ba ni da lokacin yin wasa. Dole ne in yiwa iyalina hidima. Muna buƙatar gida na zama. Shin za kiiya taimaka min?”

“Yi hakuri, amma ba ni da wani gida. Amma za ka iya sare rassana domin ka gina gidanku.” Sai mutumin ya sare rassan bishiyar ya tafi da murna. Itaciyar tayi murna da ganinshi yana murna amma mutumin bai dawo ba tun daga lokacin. Itaciyar ta sake zama cikin kaɗaici da baƙin ciki.

Wata rana zafi zafi, mutumin ya dawo kuma bishiyar ta yi murna.

“Zo ka yi wasa da ni!” bishiyar ta ce masa.

“Na tsufa. Ina so in tafi cikin jirgin ruwa don shakatawa. Za ki iya ba ni jirgin ruwa?” Inji mutumin.

“Ka yi amfani da gangar jikina don gina jirgin ka. Kana iya tafiya mai nisa kuma ku yi farin ciki.”

Sai mutumin ya yanke gangar jikin bishiyar don yin jirgin ruwa. Ya tafi cikin ruwa kuma bai daɗe da zuwa ba.

A ƙarshe, mutumin ya dawo bayan shekaru da yawa. “Yi hakuri yarona. Amma yanzu ba ni da komai da zan ba ka. Babu sauran tuffa a gare ka,” in ji bishiyar. “Ba matsala, bani da haƙoran da zan ci tuffan”.
mutumin ya amsawa Itaciyar.

“Babu sauran itacen da zan iya takawa in hau.” “Na tsufa haka yanzu” mutumin ya ce. “Ba zan iya ba ku komai ba, abin da ya rage yanzu shi ne tushena da ke mutuwa,” in ji bishiyar cikin kuka.

“Ba na bukatar abubuwa da yawa a yanzu, wurin hutawa kawai na ke so. Na gaji bayan wadannan shekaru,” mutumin ya amsa wa Itaciyar.

“Mai kyau! Tushen itacen da ya fi kyau shine wurin jingina da hutawa, ku zauna tare da ni ku huta. Mutumin ya zauna, bishiyar tayi murna tana murmushi tare da hawaye.

Wannan labarin kowa ne. Itace kamar iyayenmu ne. Sa’ad da muke ƙuruciya, muna son yin wasa da Mahaifiyarmu da Babanmu. Idan muka girma, mukan bar su; kawai ku zo musu lokacin da muke buƙatar wani abu ko lokacin da muke cikin wahala. Komai komai, iyaye koyaushe za su kasance a wurin kuma suna ba da duk abin da za su iya kawai don faranta muku rai.

Kuna iya tunanin yaron yana zaluntar bishiyar, amma haka dukanmu muke bi da iyayenmu. Mu muna daukar su a banza; ba ma jin dadin duk abin da suke yi mana, har sai ya yi latti.

~ Darasi:

Kula da iyayenku da kulawa ta ƙauna…. Domin za ka san kimarsu, in ka ga kujerarsu ta wofi…Ba mu taɓa sanin ƙaunar da iyayenmu suke mana ba; har mun zama iyaye .