Ina Jin Dadin Shan Jinin Mutane – Inji Wani Maye Da Ya Kashe Yaro 10

Jami’an an sandan kasar Kenya sun gabatar da wani matashin maye ga manema labarai bayan da ya yi ikirarin cewa ya kashe kananan yara akalla 10 ta hanyar tsotse jininsu.

Mutumin mai suna Masten Milimo Wanjala mai shekaru 20 a duniya, an kama shi ne ranar Laraba, biyo bayan gano gawarwarkin wasu kananan yara guda biyu a wata unguwa da ke wajen birnin Nairobi.

Lokacin da ake yi masa tambayoyi, Wanjala ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa ya kashe akalla mutane 10 ta hanyar tsotse masu jini, inda ya ci gaba da cewa sam ba ya nadama, saboda a cewarsa yana jin dadi a rayuwarsa idan ya tsotsi jinin mutane.

Rundunar ‘yan sandan ta ce mafi yawan wadanda mayen ya kashe yara ne ‘yan shekaru 5, 12 da kuma 13 a duniya.