Idan Na Kwanta Da Mace Mijinta Bai Kara Aure – Bokan Da Dirkawa Wata Mata Ciki

Jami’an Hisbah na Kano sun kama wani boka, Muhammad Mansur, da laifin yiwa wata mata da ta je neman magani ciki.

An kama bokan wanda ke zaune a garin Kode da ke karamar hukumar Dawakin Kudu a karamar hukumar, bayan da mai ciki wata bakwai da aka sakaya sunanta ya kai shi ofishin Hisbah domin neman a yi mata shari’a.

Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin ya shahara wajen yaudarar mata ciki har da masu aure, inda yake gaya musu idan ya kwana da su zai ba su laya da za su hana mazajen su kara mata sannan kuma su mallaki iko a kan su.

Ta shaida wa jami’an Hisbah cewa ta je neman magani a wajen bokan amma ya ce hakan ba zai yi tasiri ba har sai ya kwana da ita.

A cewar ta, mutumin ya kasance yana kokarin kwanciya da ita tun lokacin da mahaifiyar ta ta tafi tare da ita don neman magani, amma bai yi nasara ba sai da ta je can ita kadai.

“Lokacin da na raka mahaifiya ta zuwa wurin shi, ya gaya mata cewa ta zo tare da ni.”

“Wata rana na je can ni kaɗai sai ya ce dole ne ya kwana da ni kafin ya taimaka da maganin da nake buƙata. A gaskiya ma, ya ce ba zai yi aiki ba idan ba mu yi haka ba. Abin da ya faru ke nan. Ina son Hisbah su taimake ni. Ina da ciki na wata bakwai, kuma yana ƙoƙari ya ƙi, “in ji ta.

A na shi bangaren, bokan, Muhammad Mansur, ya amince da aikata laifin, inda ya kara da cewa aikin shaidan ne.

“Ta zo wurina don neman magani, amma ka san shaidan yana ko’ina idan ba ka yi hankali ba, na yarda da laifi na kuma ina son Hisbah ta yi hakuri.” Ya ce.

Sai dai kwamandan Hisbah na karamar hukumar Ustaz Kabiru Musa Dawakiji ya ce babban ofishin shi ne zai yi maganin lamarin.