“Idan Mun Ci, Ko Mu Sha” Domin Shi Ne – Inji Mahaifin Usman Da Yan Daba Suka Kashe

Mallam Abdullahi, mahaifin Usman Buda, dan shekara 25 mahaucin da aka kashe bisa zarginsa da aikata sabo a Sokoto, ya bayyana muhimmancin dansa a cikin iyalinsa.

Da yake zantawa da Daily Trust bayan Sallar Jana’izar marigayin, Malam Abdullahi ya ce, “Mun rasa mai kula da iyali, saboda shi ne duk lokacin da muka ci abinci, duk abin da muka sha shi ne ya kawo shi, babban abin da ya dame ni a yanzu shi ne, game da ’ya’yansa shida ‘yan kanana, ta yaya zan iya kula da su (’ya’yan)?

Da yake magana, Abdullahi mai shekaru 80, ya ce, “Ina kira ga Sanata Aliyu Wamakko da gwamnan jihar Sokoto da su taimaka mana domin in iya ciyar da iyalinsa.”

A ranar Talata ne aka yi jana’izar Usman Buda a Sakkwato ta hannun shahararren malamin nan na Sakkwato, Sheikh Musa Lukuwa.