Al'umma

Hotuna: Sarkin Bichi, Nasiru Ado Ya Kai Wa Shettima Ziyara

A ranar 4 ga Afrilu, 2023 Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kai ziyarar ban girma ga tsohon Gwamnan Jihar Borno da kuma sabon zababben Mataimakin Shugaban Tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima a gidansa da ke Abuja, Nigeria.

Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda ya kasance dan tsohon Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero na uku ne ya samu rakiyar wasu daga cikin ‘yan majalisarsa domin kai ziyarar ban girma ga zababben mataimakin shugaban kasa na Tarayyar Najeriya. na Najeriya, Sanata Kashim Shettima a gidansa da ke Abuja.

A yayin jawabinsa, zababben mataimakin shugaban kasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima ya yaba tare da jinjinawa Sarkin Bichi bisa ziyarar da ya kai gidansa. Ya kuma yabawa Alhaji Nasiru Ado bisa dukkan ayyukan alheri da yake yi na tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasa.

Credit: Kashim Shettima Via Facebook.