Jerin Sunayen Matan Alaafin Na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi 13

Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, daya daga cikin sarakunan (Traditional Rulers) da suka yi tasiri a kasar Yarbawa (Yoruba Landa), ya rasu ne a ranar 22 ga Afrilu, 2022, yana da shekaru 83, wanda hakan yasa ya zama Alaafin mafi dadewa a kan karagar mulki.

An ruwaito cewa ya shafe shekaru 52 akan karagar mulki.

Marigayi Alaafin of Oyo kuma ya yi kaurin suna a matsayin daya daga cikin sarakunan Najeriya da suka fi yawan mata.

Kafin rasuwar shi a watan Afrilun 2022 yana da shekaru 83, Alaafin of Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya auri jimillar mata 13 inda daya daga cikins u ƴar kabilar Igbo ce.

Hasali ma dai an san marigayi Alaafin of Oyo a matsayin Alaafin na farko da ya auri ƴar kabilar Igbo, ko kuma ya auri mata daga wajen kabilar Yarbawa.

Alaafin of Oyo ya auri wata ƴar kabilar Igbo mai suna Olori Chioma Adeyemi a shekarar 2020 a matsayin matar shi ta 13.

Jerin sunayen matan Alaafin of Oyo Oba Lamidi Adeyemi 13:

1. Olori Ayaba Abibat Adeyemi (first wife)
2. Olori Rahmat Adedayo Adeyemi
3. Olori Mujidat Adeyemi
4. Olori Rukayat Adeyemi
5. Olori Folashade Adeyemi

6. Olori Badirat Ajoke Adeyemi
7. Olori Memunat Omowunmi Adeyemi
8. Olori Omobolanle Adeyemi
9. Olori Moji Anuoluwapo Adeyemi
10. Olori Damilola Adeyemi
11. Olori Chioma Adeyemi

Ba a bayyana sunayen da sauran matan biyun da suka rage ba a halin yanzu. Rahotanni sun ce ba dukkan matan Alaafin ne ke halartar taron tare da shi ba. An kuma ruwaito cewa wasu daga cikin matan ba sa zama a fadar tare da sauran.