Hikimar Ɗan Gidan Yari

Wani tsoho Mmanomi ya rubuta wa ɗansa wasika da ke kurkuku:

“Ɗana, bana iya shuka Dankali, don ba zan iya nome gonar da kaina ba, nasan idan kana nan zaka ka taimake ni”.

Ɗan ya rubutowa mahaifin shi amsa:

“Baba kar ka yi tunanin noman filin domin a nan ne na binne duk kudin da na sata.”

‘Yan sanda suna karanta wasikar sai washegari aka nome filin gaba daya ana neman kudin, amma ba a ga komai ba.

Washe gari ɗan ya sake rubutawa mahaifinsa wata wasikar:

‘Yanzu baba zaka iya shuka dankalin ka, wannan shine mafi kyawun da zan iya yi maka daga nan. ‘