Halima: Mace Yar Shekara 25 Da Ta Haifi Jirirai 9 A Lokaci Guda

Mayu 4, 2021, za ta kasance har abada a cikin zukatan wasu ma’aurata ‘yan Mali waɗanda duniya ta canza bayan haihuwar jariran su tara a lokaci ɗaya.

Lokacin da Halima Cissé da mijin ta Kader Arby wani matukin jirgin ruwa tare da sojojin ruwa na Mali suka sami juna biyu. Samun hankalin duniya ba shine burin su na iyali ba.

Babu shakka haihuwa ce ta musamman yayin da jarirai tara da aka haifa ta hanyar C-section an haife su da wuri kuma duk sun tsira.

Likitocin sun yi amanna cewa jariran bakwai ne kuma sun firgita su a lokacin da adadin su ya kai tara a ranar da za a yi mata tiyatar.