Gwamnatin Zamfara Ta Amince Da Ɗaukar Ƴan Sa-Kai 2,800 Domin Yaki Da Ta’addanci

Domin kawo karshen ta’addanci a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya amince da daukar sabbin jami’an Civilian Joint Task Force (CJTF) guda 200 a kowace kananan hukumomi 14 da ke fadin jihar domin kara kaimi ga kokarin hukumomin tsaro.

Daukar mayakan farar hula na daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a taron majalisar zartaswa ta jiha, a gidan gwamnati dake Gusau, kwanan nan, wanda gwamnan ya jagoranta.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ya fitar a jiya, majalisar ta kuma amince da gina ajujuwa, gyare-gyare da kuma kayan aiki a wani bangare na kudirin gwamnati na bunkasa ilimi.

A cewarsa: “A kokarinsa na dakile matsalar rashin tsaro, Gwamna Lawal ya amince da daukar ma’aikata CJTF a dukkan kananan hukumomin jihar.

“Yayin da yake jagorantar taron SEC, gwamnan ya kuma amince da gina sabbin ajujuwa, gyare-gyare da kuma samar da kayayyakin da ake da su a fadin kananan hukumomi 14 na jihar.

Majalisar, The Guardian ta tattaro, ta tattauna kan rashin tsaro da tabarbarewar cibiyoyin ilimi a jihar; don haka, ta amince da daukar CJTF aiki domin kara kaimi ga kokarin sojoji da ‘yan sanda.

Gwamnan ya ce za a dauki CJTF 200 ne a kowace karamar hukuma ta jihar, inda ya ce wadanda aka dauka za a yi musu horo mai tsauri da zai taimaka musu wajen taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri don yakar rashin tsaro.

“Gwamna Lawal ya yi imanin cewa ilimi babban hakki ne ga dukkan ‘yan kasa. Gwamnatin sa ta himmatu wajen ganin kowane yaron Zamfara ya samu ilimi mai inganci.

“Gwamnati za ta gina, gyara da samar da ajujuwa 49 a Gusau, 11 a Anka, 15 a Bakura, 8 a Bukkuyum, 14 a BirninMagaji, takwas a Bungudu, takwas a Gummi, 19 a Kaura, takwas a Maru, 11 a Maradun. 42 a Shinkafi, takwas a TalataMafara, 27 a Tsafe da 11 a Zurmi,” Idris ya kara da cewa.