Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa Ta Ɗauki Mataki Akan Rubuce-Rubucen Dr. Jalo Jalingo

Asakamakon zaman da shugabanni da manyan maluma na qungiyar Jamatu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta ƙasa suka gabatar a ofishin shugaban qungiyar na ƙasa Sheikh Abdullahi Bala Lau tare da shugaban malaman ƙungiyar ta ƙasa, Dr. Ibrahim Jalo a sakateriyar ƙunyar ta ƙasa anan Abuja, ranar Laraba 5/01/2022.

Ƙungiyar ta fidda matsaya kamar haka.

1. Ƙungiyar ta bukaci Dr. Jalo da ya dakatar da tattauna wannan matsala ko rubutu akanta a shafin yanar gizo domin wannan matsala, lamari ne da ya shafi maluma da daliban ilimi. Kawota cikin al’umma ba zai haifar da komi ba sai rudani da rashin fahimta.

2. Ƙungiya ta ja hankalin dukkan maluman da ke qarqashin ta da cewa kafin su kawo wata baƙuwar matsala ta addani ko fatawa, da su fara gabatar da ita a gaban majalisa don tattaunawa a ilmance da samu matsaya kafin yadata cikin al’umma don kaucewa haddasa rudani da rashin fahimta.

3. Ƙungiyar tayi kira ga dukkan yan social media da ke qarqashin ta da su dakatar da yada wannan matsala a social media, kuma su janye ta daga shafukan su.

4. Ƙungiyar tayi kira ga al’ummar ƙasa da su mayar da hankalin su wajen addu’oin neman zaman lafiya da tsaro, wanda shi ne babban lamarin da yadami wannan ƙasa a yau.

5. Daga ƙarshe muna addu’a Allah ya qara mana son Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam (SAW) Ya kuma hadamana kan maluman mu bisa Qur’ani da sunnah.

Allah ya taimake mu.

JIBWS.