Dr. Ahmad BUK: Idan Haske Ya Gushe

A yau na rubuta wannan rubutu mai cike da alhini ba wai don malamin mu Dr Ahmad Buk wanda ya kware a fannin shari’a ya rasu ba, sai don kawai ina tsoron ko al’ummar musulmi a fadin duniya za su iya samun wanda zai maye gurbinsa.

Duk da cewa ni ban san Dr Buk a zahiri ba, kasancewar ba mu taba haduwa da shi ba, ya kasance kwararre na falsafar Musulunci kuma mai tasiri, wanda sunansa kadai ya isa a san shi, ballantana muryar shi.

Ba tare da wata shakka ba, rasuwar Sheikh Dr Ahmad Buk babban rashi ne ga iyalansa da al’ummar jihar Kano nagari da sauran al’ummar musulmi, saboda dimbin gogewa da iliminsa a Musulunci da zamantakewa.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kurakuransa, kuma ya sa aljannah firdausi ta zama makomarsa ta karshe.

Turawa ƴan uwa wannan sakon domin yiwa Mallam addu’a.

Daga: Arewa Times Hausa