Darasi Mai Muhimmanci Ga Ma’aurata

Wani mutum ya auri matar da yake ƙauna. Yana matuƙar ƙaunar ta suna zaman lafiya. Wata rana sai ta wayi gari da wani ciwo ya feso mata a fatar jikin ta gaba ɗaya. A hankali ciwo duk ya mamaye ko ina a jikin ta. Har ya zama kyawun ta (kyau) duk ya disashe….

Ana haka wata rana mutumin sai yayi tafiya. A hanyar shi na dawowa gida, sai ya gamu da hatsarin mota wanda hakan yasa ya daina gani….

Amma duk da hakan rayuwar auren su ta ci gaba kamar yadda yake a baya. Ana nan ana nan kyawun ta na ta duk ya gushe, amma makahon mijin na ta bai ma san da hakan ba domin bai nuna mata wani canji ba a rayuwar auren su saboda yadda yake matuƙar ƙaunar ta.

Ana haka wata rana sai matar ta mutu. Mutuwar ta, ta sanya shi cikin ƙunci sosai. Bayan an gama zaman makoki, sai mijin ya ƙuduri aniyar zai bar garin. Sai wani mutum daga bayan shi ya ƙira shi yace da shi: “Yanzu yaya za ka yi kana tafiya kai kaɗai ga ka makaho? Duk wannan tsawon shekaru matar ka ce take taimaka maka wajen tafiya?”. Sai yace da shi: “Ba makaho ba ne ni!!!!  kawai pretending na ke yi saboda idan ta san zan iya kallon cutar dake jikin ta, hakan zai fi mata ƙuna sama da cutar dake jikin ta. Ban ƙauna ce ta saboda kyanta ba kawai, a’a hasalima saboda halayen ta da dabi’un ta kyawawa na ƙauna ce ta, shi yasa na zama makahon gangan domin sanya ta farin ciki”…….

Ƴan’uwa masu daraja, idan muna ƙaunar mutum ƙauna ta haƙiƙa, za mu kai matuƙar ƙurewa domin sanya su farin ciki, hakan kuma wani lokacin dole mu zamto tamkar makafi domin kawar da kai daga aibun wasu domin sanya su farin ciki. Kyau yana gushewa, amma zuciya da ruhi koda yaushe ɗaya ne. Mu ƙauna ci juna ba don kyawun halitta zalla ba, mu haɗa da kyaun halaye da dabi’u.