Kada Ka Canja Halin Ka Na Kirki Koda Akan Makiyan Ka Ne

Wani mutum ya ga maciji yana konewa har lahira a cikin wuta, sai ya yanke shawarar fitar da shi daga cikin wutar. Da yayi haka, sai macijin ya sare shi ya jawo masa ciwo mai tsanani. Mutumin ya jefar da macijin a cikin wuta.

Don haka sai mutumin ya leko ya sami sandar karfe ya yi amfani da ita wajen fitar da macijin daga cikin wutar ya ceci rayuwar shi.

Wani da yake kallon yadda abin ya faru ya matso kusa da mutumin yace: “Macijin nan ya sare ka. Me yasa har yanzu kuke ƙoƙarin ceton rayuwar shi?”

Mutumin ya amsa da cewa: “Halin macijin shine yayi cizo, amma kuma hakan ba zai canza yanayi na na dan Adam ba, wato in taimaka.”

Kada ka canza yanayin ka don kawai wani ya cuce ka. Kada ku rasa kyakkyawar zuciyar ku, amma ku koyi yin taka tsantsan.

Tura wannan saƙon zuwa ga sauran ƴan uwa…