Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Thomas Partey ya Musulunta

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Thomas Partey, ya Musulunta, kamar yadda wani dan jaridar wasanni da ke zaune a Birtaniya ya ruwaito a ranar Juma’a.

Connor Humm ya ruwaito musuluntar Partey da hoton dan wasan tsakiyar Ghana rike da kur’ani. Dan wasan tsakiyar mai shekaru 28 ya koma Arsenal ta Ingila daga Atletico Madrid ta Spain a shekarar 2020.

Partey ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yan wasan Arsenal a ‘yan watannin da suka gabata yayin da Gunners ke da burin tsallakewa zuwa gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA.

Dan wasan na Ghana ya zura kwallaye biyu tare da bayar da taimako guda daya ga kungiyar Mikel Arteta, wacce ke matsayi na hudu a gasar Premier.