Dan Kwallon Jamus, Robert Bauer Ya Musulunta

Dan wasan baya na kasar Jamus Robert Bauer ya sanar da Musulunta tare da nuna jin dadinsa ga wadanda suka taimaka masa a tafiyarsa a matsayinsa na musulmi.

A kwanakin baya ne Bauer ya saka hotonsa na Instagram ya saka hotonsa yana Sallah kuma ya bayyana cewa ya shigo addinin musulunci ta hanyar matarsa da danginta.

“Ga duk mutanen da ke aiko min da sako a yau. Na shigo musulunci ta hanyar matata da danginta. An yi shekaru da yawa kuma ina godiya da ku duka don ku taimake ni kuma ku ƙarfafa ni a kan tafiya ta, “Bauer ya rubuta.

Wani sakon da Bauer yayi ya nuna ayar Alkur’ani mai girma yana cewa, “kuma yana tare da ku a duk inda kuke.” (Qur’an 57:4)