Al'umma

Dalilin Da Yasa Mace Zata Daina Jin Tsoron Kishiyar Ta

A cikin wannan maƙala zamu kawo wa yan uwa mata dalilin da zai sanya su daina jin tsoron cewa mazan su zasu ƙara aure.

  • Kin rigata shiga gidan, kin rigata zama da shi.
  • Kin fi ta sanin halayen shi, don haka zaki fi ta sanin yadda zaki zauna da shi lafiya.
  • Ke ce uwargidan shi kuma uwar ‘ya’yan shi. Ita kuwa bata da kowa a gidan.
  • Kin riga ta aure. Don haka watakila kin fi ta iya girke-girke kala-kala domin dauke hankalin maigida.
  • Kin fi ta sanin iyayen mijin ku da ‘yan uwan miji, da makwabta da abokan shi da dukkan jama’ar shi. (Ke kike da majority votes kenan).

Don haka kiyi kokari ki fita tsafta, kwalliya, hakuri, kulawa da bukatun maigida, da sanin hanyoyin tattali da zama da shi lafiya.

Daga karshe kuma kiyi kokari ki gyara duk wani kuskuren da zaki iya tunowa ya faru tsakanin ki da mijin ki tun kafin zuwanta da bayan zuwanta, sannan ki kyautata duk wani abinda ya baci atsakanin ki da iyayen shi ko dangin shi.

Kiyi kokari ki zarce ta wajen riko da addini da kyautatuwar niyya acikin zaman ki da ita. Duk wanda yafi kyautata niyya, to Allah zai zama gatan shi kuma zai isar masa bisa duk masu neman shi da sharri.

Ki guje wa daukar shawara daga miyagun kawaye. Musamman wadanda suka dade basu yi aure ba, da kuma wadanda auren su ya mutu (koda kuwa ‘yan uwan ki ne). Yawancin su munafukai ne kawai ba kaunar ki suke yi da gaske ba.

Ki guji zuwa wajen bokaye da Malaman tsibbu (Gobe da nisa), da ‘yan duba. Wallahi makaryata ne kuma mushrikai. Zasu jefa ki raramin shirka da tsafi. Su raba ki da kudin ki, su raba ki da imanin ki, shima mijin naki daga karshe ki rasa shi, ki ƙare rayuwar ki a wulakance.

Allah yasa mu dace.