Al'umma

Dalilin Da Yasa Na Shararawa Shugaban kasar Faransa Mari – Tarel

Bafaranshe nan dan shekara 20, mai suna Damien Tarel, ya bayyana wa kotu dalilin da yasa ya yanke hukuncin shararawa shugaban kasar, Emmanuel Macron mari.

Haka zalika, bayanin nasa ba iya dakatar da kotu daga yanke mishi hujuncin gidan yari na tsawon watanni hudu ba saboda marin shugaban nasa.

Duk da kasancewar jami’an tsaro, Tarel ya kaiwa shugaban na Faransa hari a lokacin da shi (Macron) ke musayar kalamai tare da sauran jama’a yayin wata tafiya a yankin Drome na Faransa.

Matashin mai shekaru 28 ya fadawa kotu a ranar Alhamis cewa ya yi tunanin wasu hanyoyin da zai kunyata Shugaban kasar kwanaki da dama gabanin ziyarar Macron a yankin.

Tarel ya ce yayi tunani game da jefa maj danyen kwai ko wani irin mai, mai tsami, kuma ya kara da cewa marin da yayi ba shine abinda ya shirya ba.

“Ina tsammanin Macron yana jagorancin lalacewar kasarmu,” kamar yadda ya fada wa kotun, a cewar BFM TV.