Al'umma

Dalilin Da Yasa Babangida Ya Soke Zaben Shugaban Ƙasa Na 1993

Ranar 12 ga watan Yunin 1993 ita ce ranar da ‘yan Najeriya miliyoyin suka fito domin zaben Moshood Abiola, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, inda ya doke abokin hamayyarsa daya tilo, Alhaji Bashir Tofa na National Republican Convention, NRC.

Zaben wanda aka ce shi ne wanda ya fi inganci a cikin kwanciyar hankali, sahihanci da adalci a tarihin kasar, wanda shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamosi Babangida ya soke.

Soke zaben ya haifar da zanga-zanga da tashe-tashen hankula na siyasa, ciki har da murabus din IBB da gwamnatin farar hula mai rauni.

A cewar Abiola, Babangida ne ya fara ba shi shawarar tsayawa takarar shugaban kasar na 1993. Ya tabo maganar ne a lokacin da aka yi jana’izar matar sa ta farko, Simbiat, a Legas a shekarar 1992.

Babangida ya shaidawa Abiola cewa dole ne ya tsaya takarar shugaban kasa saboda al’umma sun kagu su yi masa maraba a matsayin shugabansu na gaba ba.

Da aka tambaye shi dalilin da yasa ya soke zaben, Babangida yace: “Da a ce zabe ya gudana, da an yi juyin mulki wanda zai iya haifar da tashin hankali zaben.

Babangida ya bada misali da cewa akwai matsin lamba ga gwamnatin sa a ciki da wajen sojoji na a soke zaben.