Daga Kurkuku Zuwa Shugaban Ƙasa: Labarin Nelson Mandela Da Mai Tsaron Gidan Yari
“Bayan na zama shugaban kasa, sai na ce wa masu rakiya muje wani gidan cin abinci don cin abincin rana, kuma muna zuwa gidan cin abincin muka zauna, kowannen mu ya tambayi abin da yake so.
A kan teburin gaban mu, akwai wani mutum yana jira a yi masa abinci. Lokacin da aka yi masa bashi abincin, sai na ce wa wani soja na: je ka nemi wancan mutumin yazo ya zauna tare da mu. Sojan ya je ya kai masa gayyata. Mutumin ya tashi ya dauki farantinsa ya zauna kusa da ni.
Yayin da yake ci hannuwansa suna rawar jiki akai-akai, bai ɗaga kansa daga abincinsa ba. Muna gamawa yayi bankwana ba tare da ya kalleni ba na mika masa hannu ya fice.
Sojan ya ce da ni:
Mai gida, wannan mutumin tabbas yana rashin lafiya, ganin yadda hannunsa bai daina karkarwa ba yana cin abinci.
Babu shakka a’a! dalilin firgitar shi daban ne.
Sai na ce masa:
Wannan mutumin shi ne mai kula da gidan yarin da na zauna. Bayan ya azabtar da ni, na yi kururuwa da kuka ina neman ruwa sai ya zo ya wulakanta ni, yayi min dariya, maimakon ya ba ni ruwa, sai ya yi fitsari a kai na.
Ba lafiya ne baya da ba, kawai yana tsoron kada ni, a yanzu shugaban kasar Afirka ta Kudu, in tura shi kurkuku in yi masa abin da yayi mini. Amma ni ba haka nake ba, wannan dabi’a ba ta cikin halina, ballantana na rama.
“Shirin masu neman ramuwar gayya suna ruguza kasashe, masu neman sulhu suna gina al’ummomi. Ina fita daga kofa don samun ‘yanci, na san cewa idan ban bar duk fushi, ƙiyayya da bacin rai a baya na ba, har yanzu zan zama fursuna.”
– Nelson Mandela