Al'umma

Wani Matashi Ya Yiwa Budurwa Mai Awara Wanka Da Tafasasshen Man Suya A Zariya

Wani fusataccen matashi mai suna Dan Sule ya kwarawa wata matashiya mai suyar awara a gefen hanya tafasashen man gyada a fuska a garin Samaru, a Zariya, jihar Kaduna.

Wannan mummunan lamarin ya faru ne lokacin da matashin yazo yana cikin tsaka da cin awara ɗaya-bayan-ɗaya yana dangwalar yaji inda Hussaina tayi masa magana daya kawai sai cacar baki ta kaure a wannan gaɓar.

Bayan mintoci kaɗan, mutane sun shiga tsakani, suka raba su ya tafi abinsa, ashe labewa yayi ya shammaci mutanen da suka sulhunta, bayan ya dawo kawai ya daga kaskon tuyar awarar ya kwara mata man a fuska, kamar yadda wani ganau ya shaida hakan ya tabbatar.

Hussaina dai iyayanta talakawa ne kuma tana taimaka masu wajen gudanar da sana’ar awara wacce suke rufawa kansu asiri suci, su sha yayin da shiko matashin ance fitinar halin shi ne, kuma ya addabi jama’a a yankin.

Mun samu rahoton cewa ko a yan makonnin baya ya bugawa wani yaro Almakashi aka wanda yayi sanadin zama mai mutuwar “Barin Jiki”, yanzu dai magabatan Hussaina suna kira da Jama’a da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam da su shigo domin abi mata hakkin ta, a kuma kai mata agaji.