Cristiano Ronaldo Yana Ƙaunar Musulmai

Bayan aukuwar iftila’in girgizar kasa da ya faru a kasar Maroko, shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya, Christiano Ronaldo ya bada katafaren hotel dinsa na alfarma, mai suna PESTACA CR7 dake Morocco wanda yake daukar mutane kimanin 174 domin a ajiye mutanen da girgizan kasa ya raba su da muhallinsu a kasar, kuma a kyauta.

Christiano Ronaldo wanda yake yake taka leda a fagen kwallon kafa a Kasar Saudiyyah ba wannan karon bane ya fara tallafawa Musulmin da suka hadu da jarrabawa ba, ya kan ware wani kaso na dukiyarsa ya raba a Kasashen Musulmai irinsu Palasdinu, Iraqi, Libya, Syria da sauransu, kamar majiyoyi da dama suka tabbatar.

Yana daga cikin mutanen da suke shiga cikin sha’anin Musulmai da ake cutar da su a duniya saboda addininsu duk da shi din bai kasance Musulmi ba.

Hakika babu wani abu na sakayya da zamu yiwa Christiano Ronaldo mu biyashi ta amfaneshi wanda ya wuce mu yi ta yin addu’ah mu roka masa Allah Ya masa tukwici da karban kalmar shahada

Ance yanzu haka a Kasar Saudiyyah ya fara koyon sallama, ya fara koyon Larabci da wasu abubuwa da suka shafi dabi’un Musulmai ba.