Al'umma

Buhari Yayi Jajen Rasuwar Dr. Ahmad BUK

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa dangane da rasuwar Ahmad Ibrahim, daya daga cikin manyan Malaman addinin Musulunci kuma malamin Jami’ar Bayero Kano.

A cikin sakon ta’aziyyar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, shugaban kasar ya aikewa manema labarai, ya tunatar da dukkanin jawaban da yayi na hadisan Annabi Muhammad (SAW).

A cewarsa, Ahmad za a iya tunawa da shi a matsayin mutum mai inganci da ya yiwa addinin Musulunci da al’umma hidima, da kuma yadda yake da sha’awar wayar da kan jama’a.

“Hakika abin bakin ciki ne a gare mu baki daya sanin cewa Dr Ahmad masoyinmu ba ya nan. Mutum ne mai imani, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga ilimin addinin Musulunci.

“Za a rinka tunawa da yadda ya bayar da hadin kan musulmi, ilimi mai kyau da kuma hakkin mata.

“Muna mika ta’aziyyar mu tare da yi masa addu’ar samun kwanciyar hankali na har abada,” in ji shugaban.

Buhari ya tuna cewa marigayi Imam ya rubuta littafai da dama a rayuwarsa, daga cikin na baya bayan nan akwai fassarar littafin Muwatta Malik mai shekaru sama da 1,000 da ya rubuta zuwa harshen Hausa mai shafuka 1173, inda shi (Shugaba Buhari) ya gabatar da shi.

Kafin rasuwarsa Imam Ahmad ya koyar da musulmi kuma ya jagoranci Sallah sama da shekaru 30 kafin ya kafa “Darul Hadith”, ma’ana gidan hadisai na annabta.