Bikin Tsallaka Bijimin Sa Na Ƙabilar Hamer Ta Ethiopia

Al’ummar Hamer dake kudu maso yammacin kasar Habasha sun kasance suna gudanar da bikin tsallake bijimin sa kowace shekara, inda samari maza za su rika gudu suna tsallaka bayan bijimin sa har sau 7 ko 10 sau hudu ba tare da fadowa ba.

Duk wadanda suka yi wadannan zagayen ba tare da faɗuwa ba su ake dauke Maza.

Ana shafa wa bijimin san danyen kashin shanu domin yayi rantsi.