Yadda Dan Ta’adda, Bello Turji Da Mutanen Shi Ke Nuna Muggan Makamai
Shehu Sani, tsohon dan majalisar dattawan Kaduna, ya raba wani faifan bidiyo na fitaccen sarkin ‘yan fashin nan, Turji Bello, tare da mutanen shi suna harbin bindiga a wani wuri a yankin Arewa maso Yamma.
Bello shi ne shugaban kungiyar ‘yan ta’adda da ke addabar Zamfara da jihohin makwabta.
Sojoji sun kai wa shugaban ta’addanci hari a hare-hare da dama, amma a ko da yaushe yana samun tserewa. A baya-bayan nan ne sojoji suka bayyana cewa ana neman Turji Bello da wasu ‘yan ta’adda da dama.
A wata hira da aka yi da shi ‘yan makonnin da suka gabata, Turji Bello ya ce sojoji ba su da sha’awar kashe shi, kuma a kodayaushe suna kokarin tayar da shi ta hanyar jefa bam a gidansa.
A cikin faifan bidiyon da Shehu Sani ya wallafa a shafin Twitter a ranar Asabar, 24 ga watan Disamba, 2022, an ga Bello da ‘yan kungiyarsa suna ci gaba da aiki. Shugaban ‘yan ta’addan na yin waya ne a lokacin da mutanensa ke ci gaba da harba makamai.
Shehu Sani ya ce Bello da mutanensa za su bi hanyar da sauran da suka gabace su. Ya kara da cewa Najeriya za ta yi galaba a kansu.
Sai dai faifan bidiyon ya haifar da martani da dama daga ‘yan Najeriya a shafin Twitter.