Wata Uwa Ta Nemi A Daina Kiran Ɗanta ‘Ɗan Ruwa’ Saboda Siiffar Shi

Labarin wata uwa mazauniyar nahiyar Afrika a wata kasa da ake kira da Rwanda.

Kamar yadda zaku kalla a cikin wannan bidiyo dake ƙasa, wanda kuma aka fassara, bayan wannan mata ta wannan yaron mai diffa irin wacce ba’a san dan Adam da ita ba, mijinta ya kaurace mata.

Haka zalika, bai tsaya nan ba, ya gudu ya bar ta da yaron saboda irin halittar yaro wacce kuke gani anan.

Mutanan kauyen su, suma sun bi sawun mijinta na kaurace mata, har ta kai ta kawo suna kiran dan nata da sunan “Dan Ruwa” kuma basu son ganin shi.

Labarin dai dole ya sanya idaniya kuka idan ka kalla, cikin ikon Allah aka sami wasu mutane suka taimaka mata har aka kai dan kasar Indiya domin ayi mishi tiyata, Kuma bayan an kammala anyi nasara.