Ban San Mijina Zai Rayu Bayan Yayi Hatsarin Da Ya Dame Kansa Ba – Uwargida
Wata mata ta bada labarin halin da mijinta ke ciki bayan yayi mummunan hatsarin da ya kusan kashe shi. Ita dai wannan matar ta bada labarin ta ne da Afrimax English a yayin wata tattaunawa da aka yi ita, inda ta bayyana cewa da mijinta ya mutu a yau, amma Allah ya kubutar da shi.
Hadarin ya bata kan mijin nata ya matse shi.
Matar ta bada labarin duk abin da ya faru da mijinta yayin hirar.
Mijinta ya kasance mai hawan okada, kuma yana hawan okada don rayuwa. Yana da ya’ya da matar shi kuma suna zaune cikin jin dadi a matsayin iyali daya, har sai da wani hatsarin da yayi sanadin zaunar da mutumin a wuri daya har yau.
Rahotanni sun bayyana cewa, dalilin da yasa mai gidan ya samu rauni shine sakamakon hatsarin da ya afku a cikin dare daya a lokacin da yake dauke da kwastomomi a kan babur din shi.
A wannan daren yana dauke da mata guda biyu akan babur din shi zuwa inda suke. Matan suka ce masa zai tsayar da su a wani shago, da ya tsaya a shagon sai aka kulle wurin. Ya tambaye su ko ainihin wurin da zasu je ne domin wurin a kulle yake. Suka ce wurin ne, amma suna cikin yar gardama ne sai wani okada mai tsananin gudu ya tsallako daga hannun shi zuwa bangaren nasu ya buge su. Mutumin ya ji rauni sosai, amma matan ba su samu wani rauni ba.
Matar mutumin da ya’yansa suna gida sai aka yi musu kiran gaggawa. Uwargidan ta garzaya wurin da hatsarin ya afku, daga nan zuwa asibiti, amma asibitin yace su kai shi wani babban asibiti, wanda suka yi ba tare da bata lokaci ba.
Likitan ya gaya wa matar cewa mijinta ya rasa wani bangare na kokon kan shi, kuma dole ne a yi masa tiyata. Ya tabbatar wa matar cewa mijinta zai tsira bayan tiyatar. Sai matar ta yarda ta ce wa likitan ya cigaba da aikin tiyata. Bayan tiyatar, ya tsira kuma an sallame shi bayan raunin da ya samu ya warke.
A cewar matar, tace ta kashe makudan kudade wajen kula da lafiyar mijinta. Ta samu kudin ne daga sana’arta ta kifi, akwai lokacin da ta yi rashin kudi, sannan ba ta da wani zabi illa ta tambayi mutane kudi ta kafafen sada zumunta. Ta ce ba wanda ya san mijin nata zai tsira daga wannan hatsarin, duba da karyewar kan shi, kawai za ka yi tunanin ya mutu da gani.
Matsalar da take fama da ita a halin yanzu shine mijin nata ya kasa magana bayan hatsarin. Tana fatan mijinta ya fadi kalma wata rana, za ta ji dadi a ranar. Ita ce ke kula da mijinta bayan faruwar lamarin. Yana zaune a keken guragu duk yini, baya motsi kuma baya yin wani sauti ko kadan.
Wannan lamarin ya faru ne a kasar Tanzania.