Babban Darasi Kan Mutuwar Dan Wasan Barkwanci “Kamal Aboki”

Akwai darasi mai girma a kan mutuwar ɗan wasan barkwancin nan “Kamal Aboki”, wanda ya rasu jiya a wani mummunan hatsarin mota akan hanyar Kano zuwa Maidugura, jihar Borno.

Cikin bidiyoyi na shi da muka sa jiya, akwai wani da aka ɗauke shi yayi tagumi, sai wani ya tambaye shi Kamal yaya ka yi da tagumi? Sai Kamal ɗin ya ce ba dole na yi tagumi ba, Allah ya turo mu duniya don mu yi bautar shi, amma mun ɓuge da yin comedy (wasan barkwanci), sai abokan shi da ƴan matan da suke wurin suka fashe da dariya (kya-kya), sai Kamal yace wato dariya ma na ba ku da wannan maganar.

Wannan bidiyo a fahimta ta ba shiryawa a kayi ba ya faru ne a zahirin gaskiya.

Allah sarki rayuwa, yau sai ga shi ya koma ga Ubangiji, kuma Allah ya yi alƙawarin tashin kowa kan abin da ya mutu a kai, (Lailaha Illa Anta Subhaka Inni Kuntu Minaz-zalimin).

Ƴan uwa masu girma, Kamal Aboki da ire-iren shi sun san abin da suke kai ba dai-dai ba-ne amma kullum suna ɗauka wa kan su cewa zuwa wani lokaci za su bari, amma ta Allah ba ta su ba, sai mutuwa ta riga su, alhali suna rafkane.

Ƴan uwa, masu girma, jinkirin tuba ɓata ne, kowa ya duba abin da yake kai wanda ya san ba dai-dai ba ne ya gyara, sannan ya nemi gafarar Allah mai Rahama, (Allah ya kasance mai yawan gafara da rahama).

Hakika a cikin mutuwar Kamal Aboki akwai darasi mai girma ga masu hankali da hangen nesa.

Babban abin ban tsoro da firgici a wannan gabar shine; idan mutum ya mutu dukkan ayyukan da yake yi za su tsaya cak, sai wadanda suke masu gudana, kamar gina masallaci, makaranta, sukar bishiyoyi da sauran da aka yi domin neman yardar Allah, da ake amfani da su ko bayan mutuwa.

Ga masu bin bibiyar shirye-shiryen Kamal Aboki, sun san ire-iren bidiyoyi da yake dorawa a shafukan shi na TikTok, Facebook, YouTube, Instagram da sauran su.

Ya ku yan uwa masu girma, na san cewa babu wani daga cikin mu zai so a ce ire-iren waɗannan bidiyoyin sune za su zama ayyukan shi masu gudana bayan ya bar duniya.

Daga karshe ina nema wa kaina da ku gafarar Allah, da dukkan Musulmi tun zamanin Annabi Adam (A.S) har zuwa da bayan mu.

Allah ka yafe ma na, ka azurta mu da gyarawa kafin mutuwan mu.

Wasallamu alaikum….