Asalin Haɗuwar Umar Bush Da Ibrahim Da Abinda Ya Faru A Baya
Kasuwa ce ta hada Umar Bush da Ibrahim Abdullahi, kuma dalilin da yasa Bush yake girmama Ibrahim abu biyu ne.
Na farko, shi dai Umar Bush yawo yake a kasuwa ana tsokanar shi yana zagin mutane ko yaya, wasu su bashi Naira 10, k0 ko 50, amma kullum idan yazo shagon su Ibrahim mai gidan Ibrahim yana siyawa Bush abincin rana har Ibrahim da kan ahi ya fara siyawa masa abincin 500 ko fiye, shi yasa kullum sai yazo.
Na biyu duk tsokanar da ake yiwa Bush Ibrahim bai taba tsokanar shi ba, wata rana Umar yazo kasuwa mutane suke tsokanar shi kuma a wannan ranar Bush yayi zage-zage na wuce kima, wannan dalilin yasa Ibrahim yayi sha’awar yi masa bidiyo ya dora a TikTok, anan bidiyon ya shiga duniya Hausawa.
Daga nan mutane suka fara cewa ai Bush mahaukachi ne, Ibrahim da kudin aljihun shi ya fara siyawa Umar takalama da kayan sawa kuma bada niyar yayi mishi bidiyo ba kawai saboda kyautatawa.
Ana wannan hali aka ci gaba da yiwa Umar bidiyo aka fara bawa Umar kudi 1k, 2k har 5k ta hannun Ibrahim, kuma duk abinda aka samu Ibrahim yana bawa umar kudin shi daga baya aka fara tara masa.
Ibrahim yaje ya sanar da mahaifin Umar akan bidiyo da suke yi, kuma mahaifin ya amince har ya zama lokaci zuwa bayan lokaci yana zuwa ya amshi kudin da Bush ya samu a hannun mai gidan su Ibrahim na kasuwa saboda shi ake bawa ya ajiye.
Ana cikin haka Moofy da hukumar yan sanda suka sako Ibrahim gaba akan a daina yiwa Umar bidiyo amma Ibrahim ya jure kalubale da komai har sukayi nasara. Su Abba Hikima suka shigo case din amma shima Ibrahim yayi nasara, an zage shi, anci mutumcin shi duka ya jure.
Amma Abba G a cikin kwana 9 da haduwar su da Ibrahim wanda shi ya gayyace su ranar Sallah, ashe wannan bidiyon yayi amfani dashi yaje ya yaudari iyayen Umar cewa ai tare suke da Ibrahim kuma zai kai Umar wajan manyan mutane za’a samu alkhairi su kuma suka sutale Ibrahim suka basa Umar sabod yayi musu daɗin baki, dalilin yasa har aka zo matakin da ake ciki a yanzu.