Ali Nuhu Ya Yada Tsohon Hoton Su A Lokacin Yana Makarantar Sakandire

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, darakta, furodusa, marubuci, kuma jakadan tambari, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da “sarkin Kannywood,” ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, bayan da ya yada wani hoto a shafin shi na Instagram, sannan ya saka hoton na shi da abokan karatun shi na sakandire.

A cikin wannan hoton, ana iya ganin matashi Ali Nuhu wanda uba ne yanzu yana tsugunne a tsakanin abokan karatun shi na sakandare yayin da yake sanye da bakar riga da farin wando.

Yayin da yake yada hoton, Ali Nuhu yayi amfani da wani rubutu da ke cewa, “Wani babban jifa.” Duba hoton da taken da ke ƙasa.

Kamar yadda aka zata, cikin ‘yan mintoci kadan bayan Ali Nuhu ya raba wannan hoto mai cike da tarihi, dimbin masoyan shi da suka ci karo da shi a shafukan sada zumunta, musamman a shafin shi na Instagram, sun garzaya zuwa sashen sharhi tare da bayyana ra’ayoyin su.

Me za ku ce kan wannan hoton na Ali Nuhu da abokan karatun shi na Sakandare?