An Yanke Wa Yarinya Ƴar Shekara 13 Hannu Bisa Rashin Kuɗi

An yankewa wata yarinya ƴar shekara 13 hannu mai suna Fauziyya Sani sakamakon rashin kuɗin kai ta asibiti domin kula da ita a jihar Zamfara.

A wannan lokaci matuƙar kana raye Allah bai gama halittar ka ba, har sai ka koma ga Ubangiji.

Wannan yarinyar da kuke gani kamar yadda muka samu labari, sunan ta “Fauziyya Mallam Sani, ta haɗu da tsautsayi a satin da ya gabata sakamakon faɗowa da tayi daga bisa gado wanda hakan yasa ta samu karaya a hannun ta na dama wanda sanadiyyar hakan ne yasa aka yanke mata hannun bisa rashin karfin iyayenta suke fama da shi a jihar Zamfara.

A hirar ta da gidan talabijin na yanar gizo Mai-Biredi TV, Fauziyya ta bayyana cewa tun farko ɗaurin karayar gida ne da aka yi mata wanda hakan yayi sanadiyar riƙe mata jijiyoyi, wanda yasa jini baya fudanawa a sashen.

A cewar Fauziyya ta kammala karatun firamare tsawon shekara 3 da suka wuce, amma har yanzu bata samu damar ci gaba da karatu ba saboda rashin kuɗi har ya zuwa faruwar wannan mummunar jarabawar da Allah yayi mata, inda tace tana son ta ci gaba da karatu idan ta samu wanda zai taimaka mata.

Tare da; Comr Nura Siniya