An Kona Masallaci Kurmus A Jihar Gombe Akan Rikicin Nadin Sarauta

Rahotanni da muke samu daga jiya Assabar zuwa yau Lahadi sunyi nuni da cewa har yanzu tsugune bata gare ba game da wani rikicin nadin sarautar gargajiya a garin Tangale dake karamar hukumar mulki ta Billiri wanda ya rikide ya zama tashin hankali inda har ta kai an kone masallacin Ahlissunnah (Yan Izala) na garin.

Mutane da dama suna mamakin dalilin da zai sa a kona masallaci saboda nada mai Tangale.

Idan ba’a manta ba, jiya shugaban kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’a Wa’qamatus-sunnah Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi kira ga jama’an tsaro da su dauki mataki domin hans aukuwar irin abinda ya faru a jiya, kamar yanda kuke gani a cikin hotuna ga masallaci nan na ci da wuta.

Ga abinda wani dan uwa ya rubuta a shafin sa na Facebook, wanda ya nuna shima yayi tu’ammali da masallacin na tsawon shekaru;

MEYE ALAQAR NADA MAI TANGALE DA KONA MASALLACI?
WANNAN SHINE MASALLACIN KOFAR FADAN GALADIMAN TANGALE, HAKIMIN BARE BILLIRI L.G.A. DA NAYI SHEKARU GOMA (10 years) INA TAFSEERIN AL’QUR’ANI MAI GIRMA ACIKIN SA YANA CIN WUTA!!

Muna kiran Gombe State Government da Jami’an tsaro su dauki matakin gaggawa akan wannan abu kuma su tabbatar an hukunta duk mai hannu acikin wannan aiki na ta’addanci.”