Allah Ya Yafe Min, Ya Kuma Ɗora Ni Bisa Hanya Mai Kyau – Safara’u

Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa kuma mawakiyar hip-hop, Safara’u Yusuf, wadda aka fi sani da Safa, ta janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta daga mabiyan ta bayan ta wallafa wani sabon rubutu a shafin ta na Instagram, inda ta ce ta yi nadamar abin da ta aikata a baya kuma ta yi addu’a don zama mutumiyar kirki.

A cikin sakon, Safara’u, wacce ta yi fice wajen sanya kayan kwalliyar da suka bayyanar da surar jikin ta, an ganta sanye da wata babbar rigar abaya.

Ta raba hoton tare da wani taken da ke cewa, “Ina ƙoƙarin zama mutum mafi kyau; dukkan mu muna yin kuskure kuma dukkan mu muna da abubuwan da muke nadama da aikatawa kuma ina ƙoƙarin gyara kaina don fitar da ingantacciyar sigar kaina. Allah Ya gafarta mani, kuma Ya shiryar da ni tafarki mafi kyau”

Wannan rubutun ya dauki hankulan masoyanta ciki har da ‘yar wasan ta, Maryam Booth.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne Safara’u ta shiga cikin rudani a shafukan sada zumunta bayan ta watsar da wasan kwaikwayo ta kuma shiga waka tare da fitaccen mawakin Hausa hip-hop, Mista 442.