Alkalancin Shehu Jaha

Wata rana wani mutum yayo itace a daji iya kan hanyarsa ta dawowa sai suka kwance suka zube ya rasa yadda zaiyi. Sai ga wani mutum yazo zai shige, sai mai itace yace “Malam ka taimaka ka taya ni mu tara itacen nan mu daure.”

Mutumin yace “idan na taya ka me zaka ban?” mai itace yace zan baka ‘babu’.

Mutumin ya taya shi suka daure itace, mutumin yace “bani abinda kace zaka bani”

Mai itace yace “ai babu nace zan baka”

Mutumin yace “to bani babun”

Ai ko sai rikici ya balle a tsakaninsu har ta kai su ga alkali suka yiwa alkali bayani, alkalin yayi dabaransu na alkalai amma ina mutumin yace dole sai an bashi babunsa.

Sai mutane suka bawa alkali shawara a nemo Shehu domin shi kadai ne zai iya warware wannan shari’a. Aka nemo Shehu da yazo aka shimfida masa darduma ya zauna mai kara yayi bayani wanda ake kara ma yace gashi gashi.

K lo da Shehu yaji haka sai ya cewa mutumin “kanaso a baka babun ka ko?”

Mutumin ya amsa da “eh”

Kawai sai Shehu ya daga dardumar da yake zaune a kai ya cewa mutumin ya leka. Mutumin nan ya leka.

Sai Shehu yace “me ka gani?”

Mutumin yace. Babu sai Shehu yace to dau babunka kayi tafiyarka kana wahalda sharia.