Alheri Danko Ne: Yadda Rikon Amana Ya Canja Rayuwar Dan Agajin

A wurin rufe taron karawa juna sani na malamai masu gabatar da tafsiri, Daraktan Agaji na kasa Engr Mustapha Imam Sitti ya gabatar da wani dan Agaji da ya taka rawar gani yayi abin a jinjina masa akan riko da aiki da amana a irin wannan lokaci da amana ta yi karanci.

Salihu Abdul-Hadi Kankia, Jihar Katsina, Najeriya shi ne dan agajin kungiyar Izala da ya tsinci jaka cike da makuden kudane da kimanin su ya kai sama da naira miliyan dari da kari (₦100,000,000).

Salihu yaje ya ajiye kudin a gida ya garzaya, sannan kuma ya tafi zuwa ofishin yan sanda dake kusa da shi ya sanar musu cewa ya tsinci jaka ayi cigiya cikin al’umma, amma kuma shi zai ajiye jakar tana wurin shi.

Bayan an samu mai wannan jakar da ta bata, wata mata ce wacce ke kiyayya da Izala mai jakar, sannan aka damka wa mai ita, ta duba ta ga kudin ba abin da aka taba ciki, tayi murna, ta ce Allah yasa kai ba dan Izala ba ne (wato wanda ya tsinci kudin), saboda Allah ya samin kin Izala! Inji matar.

Dan agajin ya ce mata, Hajiya ba ma kawai ni dan Izala ba ne, ni dan agajin Izala ne, ya cire katin shaida ya nuna mata. Ta ce assha, yau Hajiya za ta shiga Izala ba tare da a’ta yi shiri ba.

A takaicen bayani, yanzu haka Hajiya ta ce sune yan sahun gaba-gaba a Izala saboda ta mika ma dan agajin kudi bai karba ya ce mata shi yayi don Allah ne. Ta matsa masa, amma bai ya karba.

Bisa wannan namijin kokari da wannan ɗan agajin yayi:

1. Kungiyar Izala ta karrama shi da lambar yabo, sannan an ba shi kyautar kujerar Hajjin ba na, 2024.

2. Hon. Abdulmalik Zannan Bangudu (Dan agaji, kuma Dan Majalisa a Jihar Zamfara) ya ba shi kyautar miliyan biyu (₦2,000,000).

3. Gwamnan Jihar Bauchi, Sen. Bala Abdulkadir Muhammed ya bashi kyautar mota bus don ya kama sana’a.

Ba shakka wannan dan sgaji ya fidda masu gaskiya kunya. Wannan shi ne ainihin aqidar Izala, yin aikin kirki da bin tafarkin sunnah ba wai amsawa kadai a suna ba.