Al'umma

Akwai Kalar Mutane 3 A Cikin Rayuwar Ka (Ma’anonin Su)

  1. Mutane masu kalar ganye
  2. Mutane masu kalar reshe
  3. Mutane masu kalar tushe/sanyu

Mutane kalar ganye

Waɗannan mutane ne waɗanda suka shigo cikin rayuwar ku kawai saboda da wani yanayi. Ba za ku iya dogara da su ba saboda suna da rauni. Abin da suke so kawai suke zuwa wurin shi, amma idan iska ya zo, (ma’ana lokacin tsanani) za su tafi. Dole ne ku yi hankali da irin waɗannan mutane saboda suna son ku lokacin da abubuwa suka yi kyau, amma idan iska ya zo (tsanani), za su bar ku.

Mutane kalar reshe

Suna da ƙarfi, amma kuna buƙatar yin hankali da su kuma. Suna watsewa lokacin da rayuwa ta yi tauri kuma ba za su iya ɗaukar nauyi da yawa ba. Za su iya zama tare da ku a wasu yanayi, amma za su tafi lokacin da ya yi wahala.

Mutane kakar tushe

Waɗannan mutanen suna da mahimmanci saboda ba sa yin abubuwan da za a gani. Suna goyon baya ko da ka shiga cikin mawuyacin hali za su shayar da kai kuma ba su motsawa daga matsayinka, haka kawai suke son ka. Ba duk mutanen da kuka haɗu da su ba ne za su zauna tare da ku ba a duk zamani. Mutane kalar tushe ne kawai za su tsaya ko da yanayi, iska ko nauyi.

Mutanen Reshe.