Al'umma

Aisha Tsamiya Ta Auri Alhaji Buba Abubakar

Duk da ikirarin da ta yi a ranar Alhamis cewa ba za a daura mata aure ranar Juma’a ba, an daura auren Aisha Aliyu (Tsamiya) da Alhaji Buba Abubakar.

Mujallar Fim ta ruwaito Aisha a jiya tana cewa za a daura aurenta a watan Maris ba kamar yadda aka nuna a katin gayyata ba.

Sai dai jim kadan bayan buga labarin namu a jiya, wata majiya da ke kusa da Aishar ta shaida wa mujallar Fim cewa za a daura auren ne a ranar Juma’a 25 ga Fabrairu, 2022 kamar yadda aka tsara tun farko.

Majiyar ta ce Aisha ta bayyana hakan ne a dandalinta na sada zumunta domin bata mutane.

Tabbas hakan ta faru, domin a safiyar yau aka daura auren Aisha Muhammad Ali da angonta Alhaji Buba Abubakar.

Sabanin yadda aka nuna a katin, an daura auren ne a masallacin Malam Aminu Ibrahim Daurawa da ke Kano, wato lokaci da wurin da aka daura auren.