Mijin Wata Mata Da Ta Haifi Ƴaƴa 44 Ya Tsere

Bidiyon wata mata ƴar yankin Afirka mai shekaru 40 a duniya wacce kuma ta haifi ƴaƴa 44 daga mutum ɗaya ya yaɗu a duniya.

A cikin bidiyon an nuna gidan da suke rayuwa. Matar dai ta bar mutane da yawa cikin mamaki.

An nuna hoton cikin gidan da matar ke zaune tare da yaran. Amma kuma kash! An bayyana cewa mijinta ya gudu.