Al'umma

Abubuwa 5 Da Namiji Bai Kamata Yayi Ba Domin Daɗaɗawa Mace Rai Ba

Ya ku maza, ga abubuwa guda 5 da bai kamata ku yi ba don faranta wa mace rai ba, domin zaku iya yin dana sani daga baya.

Duk yadda kake son mace akwai abubuwan da bai kamata ka taba yin komai ba da sunan faranta mata rai.

A matsayin ka na namiji kana da alhakin faranta wa matar ka rai amma a sami iyaka. Kana da manufofin da za ka kare a matsayin ka na namiji kuma kada ka bar mace ta lalatar da su ko kuma ta yi amfani da kai don kawai kana son ta.

Biya mata kudin makaranta

Sai dai idan ita ce matar ka, kada ka biya kudin karatun mace. Ba laifi a taimaka mata da tallafa mata idan tana makaranta amma biyan mata komai babban kuskure ne.

Idan ka ji dole ka yi hakan, kada ka ɗauka cewa har abada za ta ci maka bashi. Mutane suna canzawa kuma tana iya zaɓar son wani ko da bayan duk ƙoƙarin ku.

Aikin Laifi Domin Ta

Idan ba za ka iya cigaba da rayuwar ta mai kyau ba, kada ka yi sata ko yin wani abu na wauta don kawai ka faranta mata rai. Idan tana son ka da gaske, za ta fahimci lokacin da kuka rabu kuma ba za ta matsa maka don warware matsalolin ta na kuɗi ba.

Yi Mata Alƙawarin Biyan Bukatu

Sai dai idan ya zama dole, ya kamata ku zama yan son kai tare da kan ku. Ba za ka iya zama da yunwa ba don ka aika mata da kuɗin sayo abinci ba. Wataƙila kuna iya raba ɗan abin da kuke da shi amma kada ku sadaukar da duk abin da kuka samu don faranta mata rai.

Watsi Da Manufofin Ka

Kafin ku hadu da ita, ku tuna kuna da burin ku. Kada ka daina bin su don kawai ba ta son abin da kuke yi. Idan kana so ka tafi karatu a ƙasashen waje, abu na ƙarshe da kake son yi shine canza ra’ayin ka saboda ba ta gamsu da shi ba. Idan ba za ta iya jira ba, bar ta kawai, amma kada ka daina bin mafarkin ka don faranta wa mace rai.

Wulakanta Yan Uwa

Mata za su iya zama masu rikon sakainar kashi musamman idan sun san kana son su tabbas kuma za ka iya yin komai don su zauna. Wasu za su yi ƙoƙari su nuna maka yadda ’yan gidan ka suke da kyau kuma su jawo ka gaba da su. Idan ta bar ka, mutanen da za ka kasance a bayan ka su ne dangin ka. Don haka, kada ku yanke alakar dangin ku don faranta mata rai.