Al'umma

Abu 3 Da Bai Kamata Ka Fada Wa Kowa Ba Game Da Matar Ka Ko Budurwa Ba

Ga wasu sirrikan da bai kamata ka taba gaya wa kowa game da budurwar ka ko matar ka ba.

Kada ka gaya wa kowa bayan ta

Ba abu mai kyau ba ne ka yi magana game da abin da budurwar ka ta yi a baya tare da abokan ka ba. Wasu daga cikin mu sun yi abubuwan masu muni a baya. Idan ta bude maka kada ka zagaya watsa shi a waje.

Kada ka gaya wa kowa matsalar ta

Dangantakar ku wuri ne mai aminci. Kowa yana da nasa rashin tsaro. Karka bata sunan budurwa ko matar ka a bainar jama’a. Idan tana da kiba sai ka kwadaitar da ita wajen motsa jiki kada ka yi mata gori da abokan ka.

Kada ka gaya wa kowa raunin ta

Wataƙila ba ta da kyau a akan gado ko kuma ba ta san girki ba. Wannan ya kamata ya kasance tsakanin ku biyu. Nemo hanyoyin warware shi maimakon gaya wa abokan ka. Lallai zai karya mata zuciya idan ta gane.

Advertisement