Abin Sosa Rai: Wata Mata Ta Mutu Ranar Auren Ta

Wata mata ‘yar shekara 33, Nadia Joseph-Gosine, ta mutu kwatsam a safiyar ranar auren ta da abokin soyayyar ta na shekara biyar.

An tattaro cewa Nadia, daga Beckton, ta yi tafiya zuwa Trinidad don yin aure da angon ta, Devon Gosine, a lokacin da ta mutu a cikin barci saboda gazawar hanta.

Mahaifiyar daya, wacce ke Trindad tare da dan ta mai shekaru 10, Emari, sun iso ‘yan makonni da suka gabata a shirye-shiryen babbar ranar ta, amma ta mutu sa’o’i kadan kafin bikin auren ta yayin da take kwana kusa da angon ta.

‘Yar’uwar Nadia, Isha Daley, ta ce ta san Nadia tana da matsalar hanta a baya amma tana tunanin komai ya daidaita.

‘Yar’uwar Nadia, Isha Daley, ta ce ta san Nadia tana da matsalar hanta a baya amma tana tunanin komai ya daidaita. Devon, saurayin Nadia, shi ma bai san cewa ba ta da lafiya.

“Tana son yin farin ciki ne kawai. Ta yi kyau sosai. Cikakken ban mamaki. Kuma tana son rayuwa, tana son yin balaguro.” Inji ‘yar uwar ta.

Angon Nadia da ke cikin raɗaɗi, Devon, ya bayyana ta a cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da MyLondon a matsayin “wanda ya fi kowa ƙauna, kulawa, kuma na gaske” da kuma ƙaunar rayuwar shi.

“Ita ce soyayyar rayuwa ta. A koyaushe ita ce mafi kyawun sashin rayuwa ta.’ Ba zan iya daina tuna abin da ya faru ba. Ganin komai kuma har yanzu ina cikin kaduwa.

Bayan duk wannan lokacin za mu yi aure. Muna cikin shiri har karshen rayuwar mu, kwatsam sai aka dauke ta. Abu mafi wahala,” in ji shi, cikin kuka.