Abinda Ya Faru Bayan Matar Ɗan Wasan Morocco, Achraf Hakimi Ta Nemi Rabuwa Da Shi

Matar babban dan kwallon kafar Morocco, Achraf Hakimi ta shigar da karar saki kuma tana son fiye da rabin kadarori da dukiyar dan wasan kwallon kafar.

Achraf Hakimi yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi samun albashi a Ligue 1, yana karbar sama da Yuro miliyan daya a wata.

Don haka tsohuwar matar za ta sami tarin dukiya. Amma da suka isa kotu, sai suka gane cewa Achraf Hakimi ba shi da wata kadara kuma bankin ba shi da ko ɗaya. Achraf Hakimi ya dade yana sanya dukiyoyinsa a karkashin sunan mahaifiyarsa, ba tare da sanin matar shi ba.