Abin Da Baku Sani Ba Game Da Hajiya Dada, Mahaifiyar Su Ƴar Adua

Mijin ta shi ne Musa Ƴar Adua, tsohon minista ne, sannan kuma ita ta haifi tsohon mataimakin shugaban ƙasa a 1979- 1981, wato marigayi Shehu Musa Ƴar Adua.

Haka kuma Hajiya Dara ita ce mahaifiyar gwamnan da yayi shekara takwas a jihar Katsina (Umaru Musa Ƴar Adua) a 1999 -2007 daga bisani ya zama shugaban ƙasa daga shekarar 2007-2009.

Hajiya Dadace ta haifi tsohon Colonel, yanzu Sanatan Katsina, Abdul’aziz Musa Ƴar Adua.

Haka kuma jikan Hajiya Dada, yayi minista a shekarar 2009-2011 sannan kuma jikokin ta mata guda uku suna auren tsoffin gwamnoni a kasar nan, wato na Kebbi, Bauchi da Katsina.

Allah ya karawa Hajiya Dada nisan kwanaki masu albarka da lafiya.