Al'umma

2023: Shekarar Kishin Kiyashi Ga Dubban ‘Ya’yan Falasdinawa

Kungiyar kare hakkin yara ta kasa da kasa, (Defence for Children International) ta bayyana cewa an kashe akalla yara kanana Falasdinawa dubu 8,000 zuwa dubu 10,000 a zirin Gaza da kuma sama da yara 121 a yankin yammacin gabar kogin Jordan da kuma birnin Kudus a shekarar cikin shekarar 2023 kaɗai, inda ta kira wannan shekarar da “shekarar kisan kiyashi” da sojojin Isra’ila suka yi a doron kasa.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta yi nuni da cewa adadin kisan gillar da aka yiwa ‘ya’yan Falasdinawa a hannun sojojin Isra’ila a cikin shekarar da ta gabata, 2013, ba a taba ganin irinsa ba tarin duniya ba, wanda ke nuni da cewa yaran Palasdinawa ne manyan hare-haren kasar Isra’ila a Gaza.

Har ila yau, ana sa ran adadin yaran da aka kashe zai karu sosai, yayin da har yanzu dubban yara ke bacewa a Gaza, wadanda suka makale a karkashin baraguzan gidajensu da aka kai musu harin bama-bamai, jiragen yaki da ake kyautata zaton sun mutun a karkashin gine-gine a faɗin yankin Gaza.

Haka kuma, katse hanyoyin samar da abinci da ruwan sha mai kyau da wutar lantarki da magunguna ga asibitoci da man fetur da kuma ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan asibitocin da makarantu da gidajen biredi da tashohin ruwa da filayen noma ba makawa zai haifar da mutuwar kananan yara na gaba da dama saboda tsanantar yanayin.

Advertisement