Al'umma

Ƴar Najeriyar Da Ta Zama Birgediya-Janar A Rundunar Sojojin Amurka

Ba’amurkiya ƴar asalin Najeriya mai suna Amanda Azubuike ta samu ƙarin girma daga muƙamin Kanal zuwa Birgediya-janar a rundunar sojojin kasar Amurka.

Ta samu ƙarin girman ne bayan da majalisar dattawan Amurka ta amince da ita a watan Yunin 2022.

Azubuike wacce iyayen ta suka kasance ƴan Najeriya, an haife ta ne a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda ta shiga rundunar sojojin Amurka a shekarar 1994.

Da yake taya ta murnar samun ƙarin girman a wani sako da ya wallafa a shafin shi na Twitter, Manjo-janar Antonio Munera da ke jagorantar makarantar sojoji ta Amurka, yace suna farin ciki da samun matsayin a wani biki da aka yi a cibiyar sojoji a Fort Knox a Kentucy da ke kasar Amurka.