Zuba Kudi A Harkar Fina-Finai Yafi Gina Masallatai Da Makarantun Islamiyya – Momo

Sanannen jarumi a ma’aikatar shirya fina-finan hausa, wacce aka sani da (Kannywood) Aminu Sharif Momo yace a yanayin da muke ciki a halin yanzu da gina masallatai da makarantun Islamiyyoyi gwara a zuba kudaden gine-ginen a harkar shirya fina-finai ta hausa, wato (kannywood).

Wannan majiya ta Arewa Times NG ta samu wannan jawabin na Sharif Momo bayan da wani na kusa da shi ya wallafa a shafin na Facebook, mai suna “Amb Auwal Muhd Danlarabawa” a yau Alhamis.

Ga abinda Danlarabawa ya rubuta;

Fitaccen jarimi a Masana’antar Aminu Sharif Momo yace a yanayin da ake cimi a yanzu da a gina masallatai da islamiyyu gwara a zuba kudin a harkar shirya fina-finan hausa.”