Al'umma
Yaron Da Aka Naɗa Sarauta Tun Yana Ɗan Shekara 3
Yara da yawa za su yi wasanni ko kuma su yi nishaɗi a waje tare da abokan su tun suna ƴan shekara 3, amma ga Sarki Oyo Nyimba Kabamba Iguru Rukidi IV ba haka ba ne, wanda ya riga ya koyi yadda ake mulkin masarautar mai mutane fiyeda miliyan 2 tun yana ƙarami.
Rukirabasaija Oyo Nyimba Kabamba Iguru Rukidi IV, King Oyo, shine Omukama na Toro, a Uganda. An haife shi a ranar 16 ga Afrilu 1992 ga Sarki Patrick David Mathew Kaboyo Olimi III da Sarauniya Best Kemigisa Kaboyo. Bayan shekaru uku da rabi, wato a shekarar 1995, Oyo ya hau karagar mulki, ya kuma gaji mahaifinsa a matsayin sarki na 12 na masarautar Toro mai shekaru 180.