Yan Wasa Da 2 da Suka Taɓa Cin Ƙwallaye 3 A Ƙasa Da Mintuna Huɗu A Tarihi

A baya Robbie Fowler yana rike da tarihin zura kwallo mafi sauri a gasar Premier bayan da ya ci wa Liverpool kwallaye uku a ragar Arsenal a cikin mintuna 4 da dakika 33 a ranar 28 ga watan Agustan 1994.

Kusan shekaru 21 bayan haka, Sadio Mane ya zarce tarihinsa bayan ya ci wa Southampton kwallaye uku a ragar Aston Villa a cikin mintuna 2 da dakika 56 a watan Mayun 2015.

Shin wani zai karya tarihin Mane?